1 Sar 15:30-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

30. Wannan abu ya faru saboda zunubin Yerobowam da zunubin da ya sa mutanen Isra'ila su yi, ya tsokani fushin Ubangiji Allah na Isra'ila.

31. Sauran ayyukan Nadab, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.

32. Aka yi ta yaƙi tsakanin Asa Sarkin Yahuza, da Ba'asha Sarkin Isra'ila dukan kwanakin sarautarsu.

1 Sar 15