28. Duk lokacin da sarki ya shiga Haikalin Ubangiji, sai matsara su ɗauki garkuwoyin, su kuma mayar da su a ɗakin tsaro.
29. Sauran ayyukan Rehobowam, da dukan abin da ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
30. Kullum akan yi ta yin yaƙi tsakanin Rehobowam da Yerobowam,
31. Rehobowam kuwa ya rasu, aka binne shi a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Na'ama, ita kuwa Ba'ammoniya ce. Ɗansa, Abaija ya gāji sarautar.