1 Sar 1:14-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Sa'ad da kike magana da sarki, ni ma zan shigo in tabbatar da maganarki.”

15. Bat-sheba kuwa ta tafi wurin sarki a ɗakinsa. Sarki dai ya tsufa ƙwarai, Abishag, yarinyar nan daga Shunem, tana yi masa hidima.

16. Bat-sheba ta rusuna, ta gai da sarki. Sai sarki ya ce mata, “Me kike so?”

1 Sar 1