1 Sam 8:11-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ya ce musu, “Ga irin halin sarkin da zai sarauce ku, zai sa 'ya'yanku maza su zama sojojinsa, waɗansunsu za su yi aiki da karusan yaƙinsa, waɗansu su zama mahayan dawakansa, da masu kai hari musamman.

12. Waɗansu kuma zai sa su zama shugabannin mutum dubu dubu da na hamsin hamsin. 'Ya'yanku ne za su riƙa yi masa noma da girbi, su ƙera masa kayayyakin yaƙi da na karusansa.

13. Zai sa 'ya'yanku mata yin aikin turare, da dafe-dafe, da toye-toye.

14. Zai ƙwace gonakinku mafi kyau, da gonakinku na inabi, da gonakinku na zaitun, ya ba fādawansa.

1 Sam 8