1 Sam 31:11-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Da mazaunan Yabesh-gileyad suka ji abin da Filistiyawa suka yi wa Saul,

12. sai dukan jarumawa suka tashi, suka yi tafiya dukan dare. Suka ɗauko gawar Saul da gawawwakin 'ya'yansa daga kan garun Bet-sheyan. Da suka zo Yabesh sai suka ƙone su a can.

13. Suka binne ƙasusuwansu a gindin itacen tsamiya a Yabesh, sa'an nan suka yi azumi kwana bakwai.

1 Sam 31