1 Sam 31:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Filistiyawa suka yi yaƙi da Isra'ilawa. Isra'ilawa kuma suka yi gudun Filistiyawa, aka karkashe su a Dutsen Gilbowa.

2. Filistiyawa suka ci Saul da 'ya'yansa maza. Suka kashe Jonatan, da Abinadab, da Malkishuwa, 'ya'yan Saul.

3. Yaƙin ya matsa wa Saul. Maharba suka harbe shi, suka yi masa mummunan rauni.

1 Sam 31