8. Sa'an nan Abishai ya ce wa Dawuda, “Yau Ubangiji ya ba da maƙiyinka a hannunka, ka bar ni in nashe shi da mashi sau ɗaya kaɗai, in sha zararsa, in haɗa shi da ƙasa!”
9. Amma Dawuda ya ce wa Abishai, “Kada ka hallaka shi, gama wa zai taɓa wanda Ubangiji ya keɓe, ya rasa yin laifi?
10. Hakika Ubangiji zai buge shi, ko ajalinsa ya auka, ko kuwa ya hallaka a wurin yaƙi.
11. Ubangiji ya sawwaƙa in miƙa hannuna in taɓa wanda Ubangiji ya keɓe. Sai dai ka ɗauki mashin da butar ruwan da yake wajen kansa, mu tafi.”
12. Da haka Dawuda ya ɗauki mashi da butar ruwan da yake wajen kan Saul, suka tafi. Ba wanda ya gansu, ba wanda ya sani, ba kuwa wanda ya farka, gama dukansu suna barci, domin Ubangiji ne ya sa barci mai nauyi ya share su.