1 Sam 13:6-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Sa'ad da Isra'ilawa suka ga sun ƙuntata, gama an matsa su ƙwarai, sai suka ɓuya cikin kogwanni, da cikin ruƙaƙe, da duwatsu, da ramummuka, da kwazazzabai.

7. Waɗansu kuwa suka haye Kogin Urdun zuwa ƙasar Gad da Gileyad.Saul kuwa yana can a Gilgal. Dukan mutanen da suka bi shi suka yi ta rawar jiki.

8. Ya dakata kwana bakwai bisa ga adadin lokacin da Sama'ila ya ɗibar masa, amma Sama'ila bai iso Gilgal ba. Mutane suka yi ta watsewa suna barin Saul.

9. Sai Saul ya ce, “Ku kawo mini hadaya ta ƙonawa da hadayun salama.” Ya kuwa miƙa hadaya ta ƙonawa.

10. Yana gama miƙa hadayar ke nan, sai ga Sama'ila ya iso.Saul kuwa ya fita don ya tarye shi, ya gaishe shi.

11. Sai Sama'ila ya ce, “Me ke nan ka yi?”Saul ya amsa ya ce, “Don na ga mutane suna watsewa, suna barina, kai kuma ba ka zo daidai lokacin ba, ga kuma Filistiyawa sun tattaru a Mikmash.

1 Sam 13