21. Kada kuma ku ratse ku bi abubuwa marasa amfani da ba za su amfane ku, ko su cece ku ba, gama ba su da wani amfani.
22. Gama Ubangiji ya yi ƙaƙƙarfan alkawari, ba zai yashe ku ba, gama ya ɗauri aniya ya maishe ku jama'arsa.
23. Amma ni kaina, Allah ya sawwaƙa in yi wa Ubangiji zunubi ta wurin fasa yin addu'a ga Ubangiji dominku. Zan riƙa koya muku kyawawan abubuwan da suke daidai.