1 Kor 7:35-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

35. Na faɗi haka ne, don in taimake ku, ba don in ƙuntata muku ba, sai dai don in kyautata zamanku, da nufin ku himmantu ga bautar Ubangiji ba da raba hankali ba.

36. Ga zancen 'ya budurwa, wadda ta zarce lokacin aure, idan mahaifinta ya ga bai kyauta mata ba, in kuwa hali ya yi, sai yă yi abin da ya nufa, wato, a yi mata aure, bai yi zunubi ba.

37. In kuwa ya zamana ba lalle ne yă yi wa 'yar tasa budurwa aure ba, amma ya tsai da shawara bisa ga yadda ya nufa, ya kuma ƙudura sosai a ransa, a kan tsare ta, to, haka daidai ne.

38. Wato, wanda ya yi wa 'yar tasa budurwa aure, ya yi daidai, amma wanda bai aurar da ita ba, ya fi shi.

39. Igiyar aure tana wuyan mace, muddin mijinta yana da rai. In kuwa mijinta ya mutu, to, tana da dama ta auri wanda take so, amma fa, sai mai bin Ubangiji.

40. Amma a nawa ra'ayi, za ta fi farin ciki, in ta zauna a yadda take. A ganina kuwa ina da Ruhun Allah.

1 Kor 7