1 Kor 2:9-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Amma kuwa yadda yake a rubuce ke nan cewa,“Abubuwan da ido bai taɓa gani ba,Kunne bai taɓa ji ba,Zuciyar mutum kuma ba ta ko riya ba,Waɗanda Allah ya tanadar wa masu ƙaunarsa,”

10. mu ne Allah ya bayyana wa, ta wurin Ruhu, domin Ruhu shi yake fayyace kome, har ma zurfafan al'amuran Allah.

11. Wane ne a cikin mutane ya san tunanin wani mutum, in ba ruhun shi mutumin ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah.

12. Mu kuwa ba ruhun duniya muka samu ba, sai dai Ruhu wanda yake daga wurin Allah, domin mu fahimci abubuwan da Allah ya yi mana baiwa hannu sake.

13. Su ne kuwa muke sanarwa ta maganar da ba hikimar ɗan adam ce ta koyar ba, sai dai wadda Ruhu ya koyar, muna bayyana al'amura masu ruhu ga waɗanda suke na ruhu.

1 Kor 2