5. Amma duk matar da ta yi addu'a, ko ta yi annabci da kanta a buɗe, ta wulakanta shugabanta ke nan, duk ɗaya ne da an aske kanta ma.
6. In mace ta ƙi rufe kanta, to, sai ta sausaye gashinta. In kuwa abin kunya ne a yi wa mace sausaye ko kundumi, to, sai ta rufe kanta.
7. Namiji kam, bai kamata yă rufe kansa ba, tun da yake shi kamannin Allah ne, abin alfahari ga Allah kuma. Amma mace abar taƙamar namiji ce.
8. (Don kuwa namiji ba daga jikin mace yake ba, amma matar daga jikin namiji take.
9. Ba a kuma halicci namiji don mace ba, sai dai mace don namiji.)
10. Shi ya sa ya kamata mace ta rufe kanta, wato, alamar ikon namiji, saboda mala'iku.
11. Duk da haka, a cikin Ubangiji, mace ba a rabe take da namiji ba, haka kuma namiji ba a rabe yake da mace ba.
12. Wato, kamar yadda mace take daga namiji, haka namiji kuma haihuwar mace ne. Amma dukkan abubuwa daga Allah suke.
13. Ku kanku ku duba fa ku gani. Ya dace da mace ke nan ta yi addu'a ga Allah da kanta a buɗe?
14. Ashe, ko ɗabi'a ma ba ta nuna muku cewa namiji ya yi gizo, abin kunya ne ba?
15. In kuwa mace tana da gashi, ba alfarmarta ce ba? Gama don rufin kai ne aka yi mata gashin.
16. In kuwa wani yana da niyyar gardama, to, mu dai ba mu san wata al'ada ba, ikilisiyoyin Allah kuma haka.
17. A game da umarnin nan kuwa, ban yaba muku ba, taruwarku ba ta kirki ba ce, ta rashin kirki ce.
18. To, da farko dai sa'ad da kuka taru, taron ikkilisiya, na ji har akwai rarrabuwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen.
19. Don lalle ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya rarrabewa da waɗanda suke amintattu a cikinku.
20. Ashe kuwa, in kun taru gu ɗaya, ba jibin Ubangiji kuke ci ba!
21. Domin a wajen cin abinci, kowa yakan dukufa a kan akushinsa, ga wani yana jin yunwa, ga wani kuwa ya sha ya bugu.