12. Wato, kamar yadda mace take daga namiji, haka namiji kuma haihuwar mace ne. Amma dukkan abubuwa daga Allah suke.
13. Ku kanku ku duba fa ku gani. Ya dace da mace ke nan ta yi addu'a ga Allah da kanta a buɗe?
14. Ashe, ko ɗabi'a ma ba ta nuna muku cewa namiji ya yi gizo, abin kunya ne ba?
15. In kuwa mace tana da gashi, ba alfarmarta ce ba? Gama don rufin kai ne aka yi mata gashin.
16. In kuwa wani yana da niyyar gardama, to, mu dai ba mu san wata al'ada ba, ikilisiyoyin Allah kuma haka.
17. A game da umarnin nan kuwa, ban yaba muku ba, taruwarku ba ta kirki ba ce, ta rashin kirki ce.
18. To, da farko dai sa'ad da kuka taru, taron ikkilisiya, na ji har akwai rarrabuwa a tsakaninku, har na fara yarda da zancen.
19. Don lalle ne a sami tsattsaguwa a tsakaninku, don a iya rarrabewa da waɗanda suke amintattu a cikinku.
20. Ashe kuwa, in kun taru gu ɗaya, ba jibin Ubangiji kuke ci ba!
21. Domin a wajen cin abinci, kowa yakan dukufa a kan akushinsa, ga wani yana jin yunwa, ga wani kuwa ya sha ya bugu.
22. A! Ba ku da gidajen da za ku ci ku sha a ciki ne? Ko kuwa kuna raina Ikkilisiyar Allah ne, kuna kuma muzanta waɗanda ba su da kome? To, me zan ce muku? Yaba muku zan yi a kan wannan matsala? A'a, ba zan yaba muku ba.
23. Abin nan kuwa da na karɓa a gun Ubangiji, shi ne na ba ku, cewa Ubangiji Yesu, a daren da aka bashe shi, ya ɗauki gurasa,
24. bayan da ya yi godiya ga Allah kuma, sai ya gutsuttsura, ya ce, “Wannan jikina ne, wanda yake saboda ku. Ku riƙa yin haka domin tunawa da ni.”