1 Kor 10:2-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Dukansu kuwa an yi musu baftisma ga bin Musa a cikin gajimaren, da kuma bahar ɗin.

3. Duka kuwa sun ci abincin nan na ruhu,

4. duk kuma sun sha ruwan nan na ruhu. Domin sun sha ruwa daga Dutsen nan na ruhu, wanda ya yi tafiya tare da su. Dutsen nan kuwa Almasihu ne.

5. Duk da haka Allah bai yi murna da yawancinsu ba, har aka karkashe su a jeji.

6. To, ai, waɗannan abubuwa gargaɗi ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi.

7. Kada fa ku zama matsafa kamar yadda waɗansunsu suke. A rubuce yake cewa, “Jama'a sun zauna garin ci da sha, suka kuma tashi suka yi ta rawa.”

8. Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi, har mutum dubu ashirin da uku suka zuba a rana ɗaya tak.

9. Kada kuma mu gwada Ubangiji yadda waɗansu suka yi, har macizai suka hallaka su.

10. Kada kuma mu yi gunaguni yadda waɗansu suka yi, har mai hallakarwa ya hallaka su.

11. To, duk wannan ya same su ne a kan misali, an kuma rubuta shi ne don a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana.

12. Don haka duk wanda yake tsammani ya kahu, ya mai da hankali kada ya fāɗi.

13. Ba wani gwajin da ya taɓa samunku, wanda ba a saba yi wa ɗan adam ba. Allah mai alkawari ne, ba zai kuwa yarda a gwada ku fin ƙarfinku ba, amma a game da gwajin sai ya ba da mafita, yadda za ku iya jure shi.

14. Saboda haka, ya ƙaunatattuna, ku guji bautar gumaka.

15. Ina magana da ku a kan ku mahankalta ne fa, ku duba da kanku ku ga abin da nake faɗa.

1 Kor 10