Ka karɓi azurfa da zinariya a wurinsu, ka ƙera kambi, ka sa shi a kan Yoshuwa, ɗan Yehozadak, babban firist.