Zab 89:39-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

39. Ka soke alkawarinka wanda ka yi wa bawanka,Ka jefar da kambinsa a cikin ƙazanta.

40. Ka rurrushe garun birninsa,Ka mai da sansaninsa mai kagara kufai.

41. Dukan waɗanda suke wucewa za su sace masa kayansa,Maƙwabtansa duka suna yi masa ba'a.

Zab 89