Zab 89:36-41 Littafi Mai Tsarki (HAU)

36. Zuriyarsa za ta kasance kullum,Zan lura da mulkinsa muddin rana tana haskakawa.

37. Zai dawwama kamar wata,Kamar amintaccen mashaidin nan da yake a sararin sama.”

38. Amma kana fushi da zaɓaɓɓen sarkinka,Ka rabu da shi, ka yashe shi.

39. Ka soke alkawarinka wanda ka yi wa bawanka,Ka jefar da kambinsa a cikin ƙazanta.

40. Ka rurrushe garun birninsa,Ka mai da sansaninsa mai kagara kufai.

41. Dukan waɗanda suke wucewa za su sace masa kayansa,Maƙwabtansa duka suna yi masa ba'a.

Zab 89