12. Kai ne ka yi kudu da arewa,Dutsen Tabor da Dutsen HarmonSuna raira waƙa gare ka don farin ciki.
13. Kai kake da iko!Kai kake da ƙarfi!
14. A gaskiya da adalci aka kafa mulkinka,Akwai ƙauna da aminci a dukan abin da kake yi.
15. Masu farin ciki ne jama'ar da suke yi maka sujada, suna raira waƙoƙi,Waɗanda suke zaune a hasken alherinka.
16. Suna murna dukan yini saboda da kai,Suna kuwa yabonka saboda alherinka.