Zab 85:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya Ubangiji, ka yi wa ƙasarka alheri,Ka sāke arzuta Isra'ila kuma.

2. Ka gafarta wa jama'arka zunubansu,Ka kuwa gafarta musu dukan kuskurensu,

3. Ka daina yin fushi da su,Ka kuwa kawar da zafin fushinka.

Zab 85