Zab 83:10-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Waɗanda aka kora a Endor,Gawawwakinsu kuwa suka ruɓe a ƙasa.

11. Ka yi wa shugabannin yaƙinsu yadda ka yi wa Oreb da Ziyib,Ka kori dukan masu mulkinsu yadda ka kori Zeba da Zalmunna,

12. Waɗanda suka ce, “Za mu ƙwace ƙasar da take ta Allah, ta zama tamu.”

13. Ya Allahna, ka warwatsa su kamar ƙura,Ka warwatsa su kamar ciyayin da iska take hurawa.

14. Kamar yadda wuta take cin jeji,Kamar yadda harshen wuta yake ƙone tuddai,

Zab 83