Zab 8:6-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ka sa shi ya yi mulkin dukan abin da ka halitta,Ka ɗora shi a kan dukan abubuwa,

7. Tumaki da shanu, har ma da namomin jeji,

8. Da tsuntsaye da kifaye,Da dukan halittar da suke cikin tekuna.

9. Ya Ubangiji, Ubangijinmu,An san girmanka ko'ina a dukan duniya!

Zab 8