6. Sa'ad da ka fafare su, ya Allah na Yakubu,Dawakansu da mahayansu suka fāɗi matattu.
7. Amma mutane suna jin tsoronka!Wa zai iya tsayawa a gabankaSa'ad da ka yi fushi?
8. Daga Sama ka sanar da shari'arka,Duniya ta tsorata, ta yi tsit,
9. Sa'ad da ka tashi domin ka yanke hukunci,Domin ka ceci waɗanda ake zalunta a duniya.
10. Hasalar mutane ba ta ƙara kome, sai dai ta ƙara maka yabo.Waɗanda suka tsira daga yaƙe-yaƙe za su kiyaye idodinka.
11. Ku ba Ubangiji Allahnku abin da kuka alkawarta masa,Dukanku sauran al'umma da kuke kusa, ku kawo masa kyautai.Allah yakan sa mutane su ji tsoronsa,