Zab 76:10-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Hasalar mutane ba ta ƙara kome, sai dai ta ƙara maka yabo.Waɗanda suka tsira daga yaƙe-yaƙe za su kiyaye idodinka.

11. Ku ba Ubangiji Allahnku abin da kuka alkawarta masa,Dukanku sauran al'umma da kuke kusa, ku kawo masa kyautai.Allah yakan sa mutane su ji tsoronsa,

12. Yakan ƙasƙantar da shugabanni masu girmankai,Ya tsoratar da manyan sarakuna.

Zab 76