Zab 73:7-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Zuciyarsu, cike take da mugunta,Tunaninsu kuma cike suke da mugayen ƙulle-ƙulle.

8. Sukan yi wa waɗansu ba'a,Suna faɗar mugayen abubuwa,Masu girmankai ne su, suna shawaraA kan yadda za su zalunci waɗansu.

9. Sukan faɗi baƙar magana a kan Allah na Sama,Su ba da umarnai na girmankai ga mutane a duniya,

10. Har jama'ar Allah ma sukan koma wurinsu,Suna ɗokin gaskata dukan abin da suke faɗa musu.

11. Sukan ce, “Ai, Allah ba zai sani ba,Maɗaukaki ba zai bincika ba!”

12. Haka mugaye suke.Suna da dukiya da yawa, amma sai ƙaruwa suke ta yi.

13. Ashe, a banza nake kiyaye kaina da tsarki,Hannuwana kuma a tsabtace daga zunubi?

14. Ya Allah, ka sa ina shan wahala dukan yini,Kana horona kowace safiya!

15. Da na faɗi waɗannan abubuwa,Da na zama marar gaskiya ga jama'arka.

16. Don haka na yi iyakar ƙoƙari in fahimci wannan,Ko da yake ya cika wuya,

17. Sai sa'ad da na shiga Haikalinka,Sa'an nan na fahimci abin da zai sami mugaye.

18. Hakika ka sa su a wurare masu santsi,Ka sa su su fāɗi su hallaka sarai!

19. Cikin ƙyaftawar ido aka hallaka su,Suka yi mummunan ƙarshe!

Zab 73