30. Ka tsauta wa Masar, naman jejin nanMai zafin hali da yake cikin iwa,Ka tsauta wa sauran al'umma, taron bijiman nan da 'yan maruƙansu,Har dukansu su durƙusa, su miƙa maka azurfarsu.Ka warwatsar da jama'ar nanMasu son yin yaƙi!
31. Wakilai za su zo daga Masar,Habashawa za su miƙa hannuwansu sama,Su yi addu'a ga Allah.
32. Ku raira waƙa ga Allah, ku mulkokin duniya,Ku raira waƙar yabo ga Ubangiji,