Zab 66:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku yabi Allah da babbar murya ta farin ciki,Ya jama'a duka!

2. Ku raira waƙar darajar sunansa,Ku yabe shi da ɗaukaka!

3. Ku faɗa wa Allah cewa, “Al'amuran da kake aikatawaSuna da banmamaki ƙwarai!Ikonka yana da girma ƙwarai,Har maƙiyanka sukan durƙusa a gabanka don tsoro.

4. Duk wanda yake a duniya, yana yi maka sujada,Yana raira maka waƙar yabbai,Yana raira yabbai ga sunanka.”

5. Zo, ka ga abin da Allah ya yi,Ayyukansa masu ban al'ajabiWaɗanda ya aikata ga mutane.

Zab 66