Zab 51:8-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Bari in ji sowa ta farin ciki da murna.Ko da yake ka ragargaza ni,Ka kakkarya ni, duk da haka zan sāke yin murna.

9. Ka kawar da fuskarka daga zunubaina,Ka shafe duk muguntata.

10. Ka halitta tsarkakakkiyar zuciya a cikina, ya Allah,Ka sa sabon halin biyayya a cikina.

11. Kada ka kore ni daga gabanka,Kada ka ɗauke mini Ruhunka Mai Tsarki.

12. Ka sāke mayar mini da farin ciki na cetonka,Ka ƙarfafa ni da zuciya ta biyayya.

13. Sa'an nan zan koya wa masu zunubi umarnanka,Za su kuwa komo wurinka.

14. Ka rayar da raina, ya Allah Mai Cetona,Zan kuwa yi shelar adalcinka da farin ciki.

15. Ka taimake ni in yi magana, ya Ubangiji,Zan kuwa yabe ka.

16. Ba ka son sadakoki, ai, da na ba ka,Ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa.

17. Hadayata, ita ce halin ladabi, ya Allah,Zuciya mai ladabi da biyayya,Ba za ka ƙi ba, ya Allah.

18. Ya Allah, ka yi wa Sihiyona alheri, ka taimake ta,Ka sāke gina garun Urushalima.

19. Sa'an nan za ka ji daɗin hadaya ta ainihi,Da dukan hadayun ƙonawa.Za a miƙa bijimai hadayu a bisa bagadenka.

Zab 51