8. Bari in ji sowa ta farin ciki da murna.Ko da yake ka ragargaza ni,Ka kakkarya ni, duk da haka zan sāke yin murna.
9. Ka kawar da fuskarka daga zunubaina,Ka shafe duk muguntata.
10. Ka halitta tsarkakakkiyar zuciya a cikina, ya Allah,Ka sa sabon halin biyayya a cikina.
11. Kada ka kore ni daga gabanka,Kada ka ɗauke mini Ruhunka Mai Tsarki.
12. Ka sāke mayar mini da farin ciki na cetonka,Ka ƙarfafa ni da zuciya ta biyayya.