Zab 51:13-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sa'an nan zan koya wa masu zunubi umarnanka,Za su kuwa komo wurinka.

14. Ka rayar da raina, ya Allah Mai Cetona,Zan kuwa yi shelar adalcinka da farin ciki.

15. Ka taimake ni in yi magana, ya Ubangiji,Zan kuwa yabe ka.

16. Ba ka son sadakoki, ai, da na ba ka,Ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa.

Zab 51