Zab 41:10-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Ka ji ƙaina ya Ubangiji, ka maido mini da lafiyata,Zan kuwa sāka wa magabtana!

11. Zan sani kana jin daɗina,Domin ba za su rinjaye ni ba,

12. Za ka taimake ni domin ina yin abin da yake daidai,Za ka sa ni a gabanka har abada.

Zab 41