Zab 4:6-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Akwai mutane da yawa da suke cewa,“Da ma a sa mana albarka!”Ka dube mu da alheri, ya Ubangiji!

7. Farin cikin da ka ba ni mai yawa ne,Fiye da na waɗanda suke da wadataccen hatsi da ruwan inabi.

8. Da zarar na kwanta, sai barci ya kwashe ni,Kai kaɗai kake kiyaye ni sosai, ya Ubangiji.

Zab 4