Zab 34:3-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Ku yi shelar girman Ubangiji tare da ni,Mu yabi sunansa tare!

4. Na yi addu'a ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini,Ya kuɓutar da ni daga dukan tsorona.

5. Waɗanda ake zalunta suka dube shi suka yi murna,Ba za su ƙara ɓacin rai ba.

Zab 34