Zab 3:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ina da maƙiya da yawa, ya Ubangiji,Da yawa kuma sun juya, suna gāba da ni!

2. Suna magana a kaina, suna cewa,“Allah ba zai taimake shi ba!”

3. Amma kai, ya Ubangiji, kullum kana kiyaye ni daga hatsari,Kana ba ni nasara,Kana kuma maido mini da ƙarfin halina.

Zab 3