1. A gare ka nake yin addu'a, ya Ubangiji,
2. A gare ka nake dogara, ya Allah.Ka cece ni daga shan kunyar fāɗuwa,Kada ka bar magabtana su yi mini duban wulakanci!
3. Waɗanda suke dogara gare ka,Ba za su kasa yin nasara ba,Sai dai waɗanda suke gaggawa su yi maka tayarwa.
4. Ka koya mini al'amuranka, ya Ubangiji,Ka sa su zama sanannu a gare ni.
5. Ka koya mini in yi zamana bisa ga gaskiyarka,Gama kai Mai Cetona ne.Dukan yini ina dogara a gare ka.
6. Ya Ubangiji, ka tuna da alherinka da madawwamiyar ƙaunarka,Waɗanda ka nuna tun a dā.
7. Ka gafarta zunubaina da kurakuraina masu yawa na ƙuruciyata.Saboda madawwamiyar ƙaunarka da alherinka,Ka tuna da ni, ya Ubangiji!