9. Shi mai alheri ne ga kowa,Yana juyayin dukan abin da ya halitta.
10. Ya Ubangiji, talikanka duka za su yabe ka,Jama'arka kuma za su yi maka godiya!
11. Za su yi maganar darajar mulkinka,Su ba da labarin ikonka,
12. Domin haka dukan mutane za su san manyan ayyukanka,Da kuma darajar É—aukakar mulkinka.