Zab 145:11-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Za su yi maganar darajar mulkinka,Su ba da labarin ikonka,

12. Domin haka dukan mutane za su san manyan ayyukanka,Da kuma darajar ɗaukakar mulkinka.

13. Mulkinka, madawwamin mulki ne,Sarki ne kai har abada.

14. Ubangiji, yakan taimaki dukan waɗanda yake shan wahala,Yakan ta da waɗanda aka wulakanta.

15. Dukan masu rai suna sa zuciya gare shi,Yana ba su abinci a lokacin da suke bukata,

16. Yana kuwa ba su isasshe,Yakan biya bukatarsu duka.

17. Ubangiji mai adalci ne a abin da yake yi duka,Mai jinƙai ne a ayyukansa duka.

18. Yana kusa da dukan waɗanda suke kira gare shi,Waɗanda suke kiransa da zuciya ɗaya.

19. Yakan biya bukatar dukan waɗanda suke tsoronsa,Yakan ji kukansu, ya cece su.

20. Yakan kiyaye dukan waɗanda suke ƙaunarsa,Amma zai hallaka mugaye duka.

21. A kullum zan yabi Ubangiji,Bari talikai duka su yabi sunansa mai tsarki har abada!

Zab 145