13. Ka sa rumbunanmu su cikaDa kowane irin amfanin gona.Ka sa tumakin da suke cikin saurukanmuSu hayayyafa dubu dubu har sau goma,
14. Ka sa shanunmu su hayayyafa,Kada su yi ɓari ko su ɓace.Ka sa kada a ji kukan damuwa a kan titunanmu!
15. Mai farin ciki ce al'ummarDa abin nan da aka faɗa ya zama gaskiya a gare ta.Masu farin ciki ne jama'ar da Allahnsu shi ne Ubangiji!