Zab 140:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka cece ni daga mugaye, ya Ubangiji,Ka kiyaye ni daga mutane masu hargitsi.

2. Kullum suna shirya mugunta,Kullum suna kawo tashin hankali.

3. Harsunansu kamar macizai masu zafin dafi,Kalmominsu kuwa kamar dafin gamsheƙa ne.

4. Ka tsare ni daga ikon masu mugunta, ya Ubangiji,Ka kiyaye ni daga masu tashin hankali,Waɗanda suke shirya fāɗuwata.

5. Masu girmankai sun kafa mini tarko,Sun shimfiɗa ragar igiya,Sun kuma kakkafa tarkuna a hanya don su kama ni.

6. Na ce wa Ubangiji, “Kai ne Allahna.Ka ji kukana na neman taimako, ya Ubangiji!

7. Ya Ubangiji, Allahna, Mai Cetona, mai ƙarfi,Kā kiyaye ni cikin yaƙi.

Zab 140