Zab 14:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wawaye sukan ce wa kansu, “Ba Allah!”Dukansu sun lalace, sun aikata mugayen al'amura,Ba wanda yake aikata abin da yake daidai.

2. Daga Sama Ubangiji ya dubi mutane,Yă ga ko da akwai masu hikimaWaɗanda suke yi masa sujada.

3. Amma dukansu sun koma baya,Su duka mugaye ne,Ba wanda yake aikata abin da yake daidai,Babu ko ɗaya.

4. Ubangiji ya ce, “Ba su sani ba?Duk waɗannan masu aikin mugunta jahilai ne?Ta wurin yi wa jama'ata fashi suke zaman gari,Ba su yin addu'a gare ni.”

5. Amma za su razana,Gama Allah yana tare da masu yi masa biyayya.

Zab 14