2. A rassan itatuwan wardi da suke kusa da muMuka rataye garayunmu.
3. Waɗanda suka kama mu suka sa mu mu yi waƙa,Suka ce mana, “Ku yi mana shagaliDa waƙar da aka raira wa Sihiyona!”
4. Kaƙa za mu raira waƙar UbangijiA baƙuwar ƙasa?
5. Da ma kada in ƙara iya kaɗa garaya,Idan na manta da ke, Urushalima!