Zab 136:12-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Da ƙarfinsa da ikonsa ya fito da su,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

13. Shi ne ya keta Bahar Maliya biyu,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

14. Shi ya bi da jama'arsa ta cikin tekun,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

15. Shi ne ya sa ruwa ya ci Fir'auna da rundunarsa,Gama ƙaunarsa madawwamiya ce.

Zab 136