1. Isra'ila, sai ka faɗi irin muguntarDa maƙiyanka suka tsananta maka da ita,Tun kana ƙarami!
2. “Maƙiyana suka tsananta mini da mugunta,Tun ina ƙarami,Amma ba su yi nasara da ni ba.
3. Suka sa mini raunuka masu zurfi a bayana,Suka mai da shi kamar gonar da aka nome.