3. Ba a koyaushe mugaye za su yi mulki a ƙasar jama'ar Allah ba,Idan kuwa suka yi, to, ya yiwu jama'ar Allah su yi laifi.
4. Ya Ubangiji, ka yi wa mutanen kirki alheri,Su waɗanda suke biyayya da umarnanka!
5. Amma ka hukunta waɗanda suke bin mugayen al'amuransu,Sa'ad da kake hukunta wa masu aikata mugunta!Salama ta kasance tare da Isra'ila!