Zab 119:97-103 Littafi Mai Tsarki (HAU)

97. Ga yadda nake ƙaunar dokarka!Ina ta tunani a kanta dukan yini.

98. Umarninka yana tare da ni a kowane lokaci,Ya sa ni in yi hikima fiye da dukan maƙiyana.

99. Ganewata ta fi ta dukan malamaina,Saboda ina ta tunani a kan koyarwarka.

100. Na fi tsofaffi hikima,Saboda ina biyayya da umarnanka.

101. Nakan guje wa halin muguntaSaboda ina so in yi biyayya da maganarka.

102. Ban raina koyarwarka baSaboda kai ne ka koya mini.

103. Ɗanɗanon ka'idodinka akwai zaƙi,Har sun fi zuma zaƙi!

Zab 119