Zab 116:5-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Ubangiji mai jinƙai ne, mai alheri,Allahnmu mai rahama ne.

6. Ubangiji yakan kiyaye kāsassu,Sa'ad da na shiga hatsari ya cece ni.

7. Kada ki yi shakka, ya zuciyata,Gama Ubangiji yana yi mini alheri.

8. Ubangiji ya cece ni daga mutuwa,Ya share hawayena,Bai bari a kāshe ni ba.

9. Don haka nake tafiya a gaban UbangijiA duniyar masu rai.

10. Na dai yi ta gaskatawa, ko da yakeNa ce, “An ragargaza ni sarai.”

11. Sa'ad da na ji tsoro na ce,“Ba wanda za a iya dogara gare shi.”

12. Me zan bayar ga UbangijiSaboda dukan alheransa gare ni?

13. Zan miƙa hadaya ta sha ga Ubangiji,Ina gode masa domin dā ya cece ni.

14. Zan ba shi abin da na alkawartaA taron dukan jama'arsa.

Zab 116