1. Ina ƙaunar Ubangiji, saboda yana jina,Yana kasa kunne ga addu'o'ina.
2. Yakan kasa kunne gare ni,A duk lokacin da na yi kira gare shi.
3. Mutuwa ta ɗaure ni da igiyarta tam,Razanar kabari ta auka mini,Na cika da tsoro da alhini.
4. Sa'an nan sai na yi kira ga Ubangiji, na ce,“Ina roƙonka, ya Ubangiji, ka cece ni!”
18-19. A taron dukan jama'arka,A shirayun Haikalinka,A Urushalima, zan ba ka abin da na alkawarta.Yabo ya tabbata ga Ubangiji!