4. Ubangiji yake mulkin dukan sauran al'umma,Ɗaukakarsa tana bisa kan sammai.
5. Ba wani kamar Ubangiji Allahnmu.Yana zaune a can ƙwanƙolin sama,
6. Amma ya duba ƙasa,Ya dubi sammai da duniya.
7. Yakan ɗaga talakawa daga ƙura,Yakan ɗaga matalauta daga cikin azabarsu.