Zab 109:27-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. Ka sa maƙiyana su sani,Kai ne Mai Cetona.

28. Watakila su la'anta ni,Amma kai za ka sa mini albarka,Ka sa a kori waɗanda suke tsananta mini.Da ma ka sa ni da nake bawanka, in yi murna.

29. Ka sa kunya ta rufe maƙiyana,Ka sa su sa kunyarsu kamar riga.

30. Da murya mai ƙarfi zan yi wa Ubangiji godiya.Zan yabe shi a taron jama'a,

Zab 109