Zab 109:19-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Su lulluɓe shi kamar tufa,Su kuma kewaye shi kamar ɗamara.

20. Ya Ubangiji, ka sa haka,Wato ya zama yadda za a hukunta wa maƙiyana ke nan,Waɗanda suke faɗar mugayen abubuwa a kaina!

21. Amma ya Ubangiji, Allahna, ka taimake ni,Yadda ka alkawarta,Ka cece ni sabili da alherin ƙaunarka.

22. Ni talaka ne, matalauci,Na ji zafi ƙwarai a can zuciyata.

Zab 109