Zab 108:6-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ka cece mu da ƙarfinka, ka amsa addu'ata,Domin jama'ar da kake ƙauna ta sami cetonka.

7. A tsattsarkan wurinsa, Allah ya faɗa ya ce,“Da nasara zan raba Shekem,Da nasara kuma zan rarraba Sukkot ga jama'ata.

8. Gileyad tawa ce, har da Manassa ma,Ifraimu ne kwalkwalina,Yahuza kuma sandana ne na sarauta.

Zab 108